Merkel, ta kai ziyarar aiki ga sarki Salman na Saudia
A yau lahadi, Waziriyar Jamus Angela Merkel ta ziyarci kasar Saudi Arabiya, ziyarar da aka sadaukar kan huldar dake tsakanin Berlin da katafariyar masarautar mai arzikin man fetur a duniya.
Wallafawa ranar:
Wannan ziyara dai tazo ne a yayinda ake shirin gudanar da zaman taron kungiyar G20 ta kasashe masu karfin tattalin arziki su 20 a watan yulin wannan shekara a Hambourg na kasar Jamus, kamar yadda majiyar diflomasiyar Jamus ta sanar.
Jim kadan bayan isarta a birnin Jedda dake yammacin kasar ta Saudiya, Merkel ta samu tarbe daga sarki Salman daya daga cikin manyan abukan kawancen jamus.
Wata majiyar ta ce, shuwagabannin 2 sun tattauna ne, kan maudu’an da zaman taron gugun g20 zai maida hankali a kai, wadanda suka hada da maganar yaki da dumamar yanayi, da kuma ta makamashi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu