Isa ga babban shafi
Kamaru

Gwamnatin Kamaru ta maidawa yankin Baminda layin Internet

Gwamnatin kasar Kamaru ta sanar da maida layin sadarwar internet a yankin kasar da ke amfani da harshen Ingilishi, watanni 3 bayan da ta yanke sadarwar bayan tarzomar da ta tashi a yankin ta adawa da gwamnatin shugaban kasar Paul Biya.

Gwamnatin Kamaru ta maida layin sadarwar Internet a yankin Baminda na Kamaru.
Gwamnatin Kamaru ta maida layin sadarwar Internet a yankin Baminda na Kamaru. REUTERS/Kacper Pempel/Files
Talla

A watan Oktoban bara ne dai mutanen yankin Baminda suka fara zanga zangar nuna adawa da yadda suka ce gwamnatin Kamaru na fifita yankunan da ke amfani da Faransanci a kansu, lamarin da ya nuna rabuwar kan da ke tsakanin yankunan kamaru biyu da kasashen Faransa da kuma Birtaniya sukai wa mulkin mallaka.

Akalla masu zanga zanga 6 jami’an tsaron kasar suka harbe yayinda suka kame wasu daruruwa, tun bayan fitowar dimbin jama’ar yankin don yin zanga zangar.

Bayan yakin duniya na daya ne majalisar dinkin duniya a waccan lokacin ta mallakawa kasashen Faransa da Birtaniya yankunan kasar Kamaru, wadanda a baya suke karkashin kasar Jamus a dunkule.

Bayan samun ‘yancin kai a shekara ta 1960, mafi rinjayen al’ummar yankin da ke amfani da harshen turanci suka zabi kasancewa cikin Kamaru a maimakon Najeriya, sai dai kuma tun a waccan lokacin suka fara kokawa bisa cewar ana nuna musu wariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.