Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru ta cafke masu zanga-zanga 100

Gwamnatin Kasar Kamaru ta ce ta kama mutane kusan 100 da suka shiga wata zanga zanga don adawa da yadda ake nunawa masu amfani da harshen Ingilishi bambanci a kasar.

Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Masu Zanga-zangar dai na adawa ne da amfani da Faransanci a Kotu da Makarantu musamman a yankunan da galibi ake magana da Inglishi.

Ministan sadarwa Issa Tchiroma Bakary ya ce wasu bata-gari sun yi amfani da zanga-zangar wajen fasa shagunan jama’a a garin Bamenda suna sace kayan da ke ciki.

Rahotanni sun ce masu zanga zangar sun bukaci samun ‘yancin kai da kuma kawo karshen mulkin shugaba Paul Biya wanda ya kwashe shekaru 34 kan karagar mulki.

Kamaru ta kafu ne dai tsakanin yankunan da turawan Faransa da Birtaniya suka yi wa mulkin mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.