Isa ga babban shafi
Kamaru

Za a binciki musabbabin hadarin jirgin Kamaru

Hukumomin Kasar Kamaru sun ce za su gudanar da bincike don gano dalilin hadarin jirgin kasan da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 70. 

Hadarin jirgin kasa na Kamaru ya lakume rayuka fiye da 70
Hadarin jirgin kasa na Kamaru ya lakume rayuka fiye da 70 STRINGER / AFP
Talla

Kamfanin da ke kula da jiragen Camrail, wanda wani reshe ne na kamfanin Bollore na Faransa ya ce, ya zuwa yanzu ba a gano abin da ya haifar da hadarin ba.

Baya ga rayukan da  hadarin ya lakume, akwai akalla 600 da suka samu raunuka daban daban.

Tuni dai shugaban kasar Paul Biya ya ayyana zaman makoki na kwana guda don juyayin wannan mummunan hadarin jirgin kasan da ya auku a ranar jumma'a da ta gabata bayan kauce daga kan layinsa a lokacin da ya ke hanyarsa ta zuwa Douala daga Younde babban birnin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.