Isa ga babban shafi
Libya

Ana cinikin ‘Yan ci-ranin Afrika a matsayin bayi a Libya

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana cinikin ‘Yan ci-rani daga Afrika da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai a matsayin bayi a Libya akan kudin da bai taka kara ya karya ba.

Dubban 'Yan ci ranin Afrika ake yin cinikinsu a matsayin bayi a Libya
Dubban 'Yan ci ranin Afrika ake yin cinikinsu a matsayin bayi a Libya REUTERS
Talla

Hukumar ta ce duk da ‘yan ciranin sun biya kudi ga masu fataucinsu zuwa Turai amma ana garkuwa da su har sai an tursasa ma su kiran iyayensu a gida domin biyan kudaden fansa.

Hukumar ta IOM ta ce kasuwar cinikin ‘yan ci ranin a matsayin bayi na neman zama ruwan dare ga wasu gungun miyagu ‘yan tawaye da ke cin karensu ba babbaka

Babban jami’in hukumar a Libya Othman Belbeisi ya shaidawa manema labarai a Geneva cewa matsalar ta yi kamari a Libya inda ake cinikin ‘yan ci rani kamar gwanjo akan farashin kudi dala 200 zuwa 500.

Sannan wasu ‘yan ci ranin a kyauta ‘yan tawayen ke sayar da su.

Mista Belbeisi ya ce wasu ‘yan ci ranin na tserewa bayan sun shafe watanni a matsayin bayi.

Masu fatauci ke yaudarar ‘yan ci ranin da sunan tsallakawa da su Turai amma da sun iso Libya sai a yi cinikinsu a matsayin bayi.

Mafi yawancin ‘yan ci-ranin ‘yan Najeriya ne da Ghana da Gambia da ke kwarara ta Libya da nufin ratsa tekun Bahrum zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.