Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Congo ta haramta gudanar da zanga-zanga

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta haramta gudanar da zanga-zangar da ‘yan adawa suka bukaci a yi a wannan litinin a duk fadin kasar.

Gwamnati Congo ta haramta gudanar da zanga-zanga
Gwamnati Congo ta haramta gudanar da zanga-zanga
Talla

‘Yan adawar dai na zargin shugaba Kabila da kasancewa kadangaren bakin tulu da ke kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya a kasar, bayan da shugaban ya ki nada wanda suke so a matsayin sabon firaminista, to sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan kasar Pierrot-Rombaut Mwanamputu ya gargadi jama’a da ka da su fito zanga-zangar domin kuwa za’a yi anfani da doka a kansu.

Shugaba Kabila dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga al’ummar kasar da suka bukaci ya yi murabus tun bayan da ya sanar da bukatar yin tazarce bayan cikar wa’adin mulkinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.