Isa ga babban shafi
DRC

Kabila zai nada sabon Firaministan Congo cikin sa'oi 48

Shugaban Jamhuriyar Demokradiyar Congo Joseph Kabila ya yi alkawarin nada daya daga cikin ‘yan adawar kasar a matsayin sabon Firaminista nan da kwanaki biyu masu zuwa, kamar yadda aka shata a yarjejeniyar da gwamnati ta cimma da ‘yan adawar a cikin watan Disamban bara. 

Shugaba Joseph Kabila tare da 'yan adawa a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Demokradiyar Congo
Shugaba Joseph Kabila tare da 'yan adawa a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Demokradiyar Congo REUTERS/Kenny Katombe
Talla

A wani jawabi da aka dauki lokaci ana dakon ya gabatar a gaban ‘yan Majalisar Wakilai da Dattijai, shugaba Joseph Kabila ya ce, zai nada sabon Firaministan Jamhuriyar Congo cikin sa’oi 48.

Wasu Limaman Cocin Katolika ne suka jagoranci cimma yarjejeniyar da zimmar kawo karshen rikicin da kasar ta tsinci kanta a ciki tun bayan da shugaba Kabila ya ki amince wa ya sauka daga mulki duk da karewar wa’adinsa na biyu kuma na .

Yarjejeniyar ta bai wa Kabila damar ci gaba da jan ragamar kasar kafin gudanar da zabe a karshen wannan shekara ta 2017.

Mutuwar jagoran ‘yan adawar Jamhuriyar Congo Etienne Tshisekedi a farkon watan Fabairun da ya gabata, ta kawo tsaiko wajen aiwatar da yarjejeniyar.

A yayin gabatar da jawabin a birnin Kinshasa, shugaba Kabila ya bukaci ‘yan adawar da su magance barakar da ke tsakaninsu, sannan kuma su mika ma sa sunayen wadanda suke so ya zaba daya daga cikinsu don nada shi mukamin Firaminista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.