Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta yi watsi da zarge zarge 6 akan Shugaban Biafra

Babbar kotun Tarayya da ke birnin Abuja a Najeriya, ta soke zarge-zarge 6 cikin 11 da ake yi wa shugaban masu gwagwarmayar kafa kasar Biafra Namandi Kanu da wasu mutane uku.

Shugaban masu fafutikar kafa kasar Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu
Shugaban masu fafutikar kafa kasar Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Mai shari’a Binta Nyako da ta yi watsi da zarge-zargen ta ce babu kwararan shedu da ke tabbatar da su.

A ranar 8 ga watan Nuwamban bara ne aka sake gurfanar da Kanu da mutanen uku a gaban kotun saboda zargin su da aikata laifukan da suka hada da ta’addanci da cin amanar kasa da kuma mallakan makamai ba bisa ka’ida ba.

Kanu dai na fuskantar tuhumar cin amanar kasa ta hanyar yada farfagandar ballewa daga Najeriya Kuma ya taba cewa kasar Biafra zata tabbata ko an kashe shi.

Fafutikar kafa kasar Biafra ya taba jefa Najeriya cikin yakin basasa a 1967 zuwa 1970 al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin Miliyan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.