Ban yi nadama ba, inji Shugaban Biafra
Shugaban masu da’war tabbatar da kasar Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa bai yi nadama ba akan dalilin da ya sa ake tsare da shi a gidan yari.
Wallafawa ranar:
Kanu ya ce sai hakar shi ta cim ma ruwa na kafa kasa mai cin gashin kanta a Najeriya.
AFP ya samu zantawa da Nnamdi Kanu ne ta hanyar dan uwan shi Prince Emmanuel Kanu a gidan yarin Kuje inda ake tsare da shi, kuma ya ce suna nan kan bakarsu ta kafa kasar Biafra.
Kanu dai na fuskantar tuhumar cin amanar kasa ta hanyar yada farfagandar ballewa daga Najeriya.
A cewar Kanu, kasar Biafra zata tabbata ko an kashe shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu