Tshisekedi Madugun adawar Congo ya rasu
Tsohon Firaministan Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, kuma shugaban madugun adawar kasar Etienne Tshisekedi ya rasu a wani asibitin Brussels yana da shekaru 84 a duniya.Tshisekedi ya taka gagarumar rawa wajen yaki da mulkin kama karya a Congo tun lokacin mulkin shugaba Mobuto Sese Seko.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tun zamanin mulkin Mobutu Sese Seko, Tshisekedi ke gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiya a Congo.
Ya rike mukamin Firaminista a karkashin Gwamnatin shugaba Mobuto Sese Seko har sau hudu, ya taka gagarumar rawa wajen yaki da mulkin kama karya a tarihin Congo, da ta yi fama da yakin basasa da juyin mulki da kuma mulkin kama karya.
Ya fara zama minista a karkashin gwamnatin Mobuto kafin ya taimaka wajen kafa Jam’iyyar UDPS a shekarar 1982 lokacin da ake kiran kasar Zaire.
Sau hudu Mobuto na nada shi Firaminista a shekarar 1990 amma kuma ba ya wuce watanni, saboda yadda manufofinsa ke karo da na shugaba Mobuto.
Tshisekedi ya yi gwagwarmaya da shugaba Laurent kabila a shekarar 1997 da kuma dansa wanda ya hau karagar mullki a shekarar 2001.
A tattaunawar neman warware rikicin siyasar kasar, an sake shirya ba shi mukamin Firaminista dan shirya yadda shugaba kabila zai bar mulki a wannan shekarar, kafin tafiyarsa Belguim dan duba lafiyarsa, kuma a can Allah Ya karbi ran sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu