Isa ga babban shafi
AU

Mahamat ya zama sabon shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU

Kungiyar tarayyar Afrika AU, ta zabi ministan harkokin wajen Chadi, Moussa Faki Mahamat, a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar kungiyar.

Sabon shugaban kungiyar tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat
Sabon shugaban kungiyar tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat
Talla

Bayan fafatawa da yan takara 4, daga karshe Moussa Faki Mahamat ya lashe zagayen karshe na zaben, inda suka fafata da ‘yar takara daga kasar Kenya Amina Mohamed, kamar yadda tsohon shugaban kasar Burundi Pierre Buyoya, dake halartar taron a matsayin babban wakilin kungiyar a Mali da yankin sahel, ya sanar.

Moussa Faki da aka zaba a wa’adin shekaru 4 zai gaji yar kasar Afrika ta kudu uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma ne, wadda aka yabawa kan yadda ta tsaya kai da fata wajen gabatar da bukatun samar da ‘yancin mata a kan teburin kungiyar, amma kuma take shan suka kan kasa aikata katabus wajen samar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar ta afrika

Fadar shugabnacin kasar Kenya ta ce, sai da aka yi zagaye 7 kafin raba gardama tsakanin ‘yan takarar neman mukamin su 5.

Sabon shugaban kungiyar ta tarayyar Afrika AU dan shekaru 56 a duniya yardajje ne ga shugaban kasar Tchadi Idriss Déby Itno, dake taka muhimmiyar rawa a cikin kungiyar ta AU wanda shima a jiya litanin ya kawo karshen shugabancin karba karbar kungiyar, tare da baiwa takwaransa na kasar Guinee Alpha Condé jan ragamar shugabancin kungiyar.

Tun a shekara ta 2008 Mahamat ke a matsayin Ministan harkokin waje na kasar Chadi, sai a yanzu da aka zabe shi a matsayin sabon shugaban kungiyar tarayyar Afrika AU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.