Gargadi daga hukumar dake kula da bakin haure
Hukumar dake kula da bakin haure ta duniya, OIM, ta ce alkallumar bakin da suka mutu a tekun Mediterranean a wannan shekarar ya zarta dubu 7, karin kashi 20 kan alkallumar shekara ta 2015.
Wallafawa ranar:
Hukumar da ke gargadi a wata sanarwa data fitar, ta ce kafin shekarar nan ta kare akwai yiwuwar wasu bakin haure ko ‘yan gudun hijira 200 zuwa 300 da su rasa rayukansu, muddin lamarin ya ci gaba kamar yadda ake a yanzu.
Kungiyar tarayyar Turai na ci gaba da yi kira zuwa Gwamnatocin kasashen Afirka na ganin sun bayar da hadin kai don cimma nasara wajen kawo karshen wannan al'amari dake ci gaba da haifar da mutuwar da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu