Isa ga babban shafi
Algeria

Kungiyoyin kare bakin haure sun nuna damuwa zuwa Algeria

Hukumomin Algeria na ci gaba da tisa keyar bakin haure zuwa garin Tamarraset dake iyaka da Jamhuriyar Nijar,Rahotanin baya baya nan na nuni cewa dubban bakin haure ne yanzu haka aka dawo da su a garin Agadez, 

Wasu daga cikn bakin haure dake kokarin tsallakawa
Wasu daga cikn bakin haure dake kokarin tsallakawa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Kungiyoyin kare hakin bakin haure na shirye domin aikewa da wasika zuwa hukumomin Algeriya a cewar Ousmane Diarra shugaban wata kungiyar dake kare bakin haure a Afrika .
Tun farko watan Disemba nan ne hukumomin Aljeriya suka kaddamar da shiri na kama duban bakin haure da suka futo daga sassan kasashe.
Akwai yan kasashe da dama ,duk da yake rahotani da kungiyar keda su na nuni cewa akwai yan kasar Mali 260 daga cikin mutane 1400 da jami’an tsaro suka kama a garin Tamarrasset.
Yanzu haka sun kama hanya zuwa garin Agadez daga Tamarrasaset, inda bayan sun samu isowa garin Agadez daga Algeria za su kama hanya gadan gadan na komawa kasashen su na asali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.