Sabon Shugaban Gambia ya cire Kalmar Islam daga jerin sunan kasar
Sabon Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya tsame Kalmar 'Islama' daga cikin sunan da ake kiran kasar ta su.
Wallafawa ranar:
A tattaunawa da manema labarai karon farko Adama Barrow ya kuma ce za'ayi sauye-sauye sosai wajen harkokin tsaron kasar, yayinda ‘yan jaridu za su sami ‘yancin walwala sosai.
Ya ce zai sauya sunan Hukumar tsaron kasar, wadda ta kunshi ‘yan sandan da ake jin tsoro saboda karfin iko da aka basu.
A shekara ta 2015 ne dai tsohon shugaba Yahya Jammeh ya sauya yadda ake kiran sunan Gambia ta zama janhuriyar Islama ta Gambia
Kashi 90% daga cikin mutan kasar dai musulmi ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu