Isa ga babban shafi
Gambia

Jammeh ya fice daga Gambia

Shugaba Yahya Jammeh na Gambia ya fice daga kasar jiya Asabar daga babban filin tashin jiragen kasar na Banjul.

Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh yayin barin kasar daga filin jiragen sama na Banjul
Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh yayin barin kasar daga filin jiragen sama na Banjul STRINGER / AFP
Talla

Tawagar manyan jami’ai hadi sojoji karkashin shugaban kasar Guinea Alpha Conde, suka yiwa Jammeh rakiya zuwa jirgin da fice da shi, zuwa inda ba’a bayyana ba.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata Yahya Jammeh ya sanar da amincewa ya sauka daga mulki tare da ficewa daga kasar, yayin jawabin da ya gabatar ta wata kafar talabijin ta kasar.

Daga cikin batutuwan da aka cim-ma yejejeniya kafin Jammeh ya amince da mika mulki akwai batun ba shi kariya da iyalansa da kuma ‘yan uwansa.

Tuni Adama Barrowa ya yi kira zuwa ga al'ummar kasar da sukayi hijira saboda fargabar tashin hankali su koma gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.