Isa ga babban shafi
Nijar

‘Yan Nijar mazauna ketare na son a dama da su a gwamnati

‘Yan Nijar mazauna kasashen ketare sun ce suna bukatar samun dama daga bangaren gwamnati domin damawa da su a lamurran da suka shafi tafiyar da kasar a fannonin ci gaba da dama.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou France 24
Talla

A zaben da ya gabata an bai wa ‘yan kasar da ke zaune a kasashen ketare damar jefa kuri’a har ma da tsayar da ‘yan takarar domin shiga a majalisar dokokin kasar a karo na farko.

Alhaji Abubakar Khalidu shugaban ‘yan Nijar mazauna Najeriya, ya shaidawa RFI Hausa cewa akwai rawar da za su iya takawa domin samar da ci gaba matukar gwamnati za ta saurare su.

A can baya dai gwamnatin Nijar ta taba cewa ‘yan kasar mazauna kasashen waje kamar wata jiha ce a cikin Nijar bayan jihohin kasar 8, amma Alhaji Khalidu ya ce har yanzu ba su ga komi ba.

Akwai dai dubban ‘Yan Nijar a makwabta Najeriya da Benin da Togo da Ghana da kasashen ketare da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.