Isa ga babban shafi
EU-Nijar

EU za ta tallafa wa Nijar saboda bakin-haure

Kungiyar kasashen Turai ta yaba wa kasar Nijar kan gagarumar rawar da ta ke takawa wajen dakile bakin hauren da ke yunkurin ratsa kasar zuwa nahiyar Turai. Wannan ya sa Kungiyar za ta duba yadda za ta taimaka wa kasar a yau Alhamis da agaji ganin yadda ta dakile bakin hauren daga dubu 70 a watan Mayu zuwa dubu 1 da 500 a watan Nuwamba. 

Wasu daga cikin bakin haure daga nahiyar Afrika da suka shiga Turai
Wasu daga cikin bakin haure daga nahiyar Afrika da suka shiga Turai Foto: Reuters
Talla

EU ta yaba wa kasar ce a lokacin da shugaba  Mahamadou Issofou ya ziyarci cibiyarta da ke Brussels kafin fara taron da za ta gudanar a yau.

Kungiyar na bukatar taimakon kasashen Nijar da Habasha da Najeriya da Mali da Senegal don ganin sun taimaka wajen hana bakin hauren tsallakawa nahiyar Turai.

Bakin daga Afrika ta Yamma na amfani ne da Jamhuriyar Nijar zuwa Libya da kuma tsallakawa ta tekun meditaraniya, in da masu safarar baki ke sanya su cikin jiragen ruwa marasa inganci suna jefa rayuwarsu cikin hadari zuwa kasar Italiya.

Kungiyar ta ce, Nijar ba wai kawai ta rage bakin ratsawa ta cikin kasar ta ba ne, ta kuma taimaka wajen mayar da baki dubu 4 da 430 zuwa kasashensu.

Kungiyar ta ce, ta tanadi karin euro miliyan 500 don bai wa kasashen na Afirka guda biyar agaji saboda rawar da suke takawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.