Isa ga babban shafi
Nijar

An bude Kokuwar gargajiya a Nijar

A yau Litinin ake soma fafatawa a kokuwar gargajiya a Jamhuriyyar Nijar bayan an gudanar da bikin bude gasar kokuwar a jiya Lahadi. A bana ana gudanar da kokuwar ne karo na 38 a Jihar Tawa.

Mutanen Nijar sun fi daraja Kokuwa fiye da kwallon kafa
Mutanen Nijar sun fi daraja Kokuwa fiye da kwallon kafa RfI Hausa/Awwal
Talla

Gasar ta kunshi ‘yan kokuwa daga jihohin Nijar 8 inda ko wace jiha ke zuwa da ‘yan kokuwa 10.

Jimillar ‘yan 80 ke fafatawa a kokuwar inda cikinsu ne za a samu Sarki wanda zai karbi takobi da makudan kudi.

Isaka Isaka na Dosso ne Sarkin Kokuwar wanda ya lashe Takobi a Dosso a bara da kuma Agadez a 2014.

Kokuwar dai ta kasance babban wasan mutanen Nijar da suke sha’awa fiye wasan kwallon kafa.

Kokuwar kuma yanzu ta koma sana’a ga wasu matasan Nijar saboda alherin da ake samu a kokuwar.

Sai dai kafin soma kokuwar ta bana akwai wasu mambobin kwamitin koli guda biyu na Kokuwar da aka dakatar na tsawon watanni shida akan rashawa.

Ana zarginsu ne da yin coge a kokuwar musamman wajen hada baki da dan kokuwa ya amince a kada shi musamman idan matacce ne a lokacin da yak e fafatawa da Dan kokuwa mai rai wato wanda ba a kada ba.

A bana an dauki matakai masu tsauri akan wannan matsalar musamman akan ‘yan kokuwar da kuma alkalan kokuwar game da coge.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.