Shirin sasanta rikicin Jamhuriyyar Demokradiyar Congo ya ci tura
Kokarin cimma matsaya tsakanin gwamnatin Jamhuriyyar Demokaradiyar Congo da 'yan adawa don ganin an bar Shugaba Joseph Kabila ya ci gaba da mulki ya ci tura, ganin zaman da bangarorin biyu suka kwashi dogon lokaci suna yi ya gagara samar da mafita.
Wallafawa ranar:
Masu shiga tsakani sun yi fatan warware matsalar kafin soma bukukuwan krismeti gudun kada rikicin kasar ya rikide zuwa yakin basasa.
Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa mutane arba’in ne suka mutu a rikicin da ya barke bayan da shugaba Kabila ya ki amincewa da sauka daga karagar mulki bayan da wa’adin mulkinsa ya shude.
Shugaba Joseph Kabila dai ya ci gaba da zama a karagar mulki duk da cewa kudurin dokar kasar bai ba shi damar sake neman mulki a wa'adi na uku ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu