Isa ga babban shafi
Masar

Kotu ta sake soke hukuncin daurin rai da rai kan Morsi

Kotun daukaka kara a Masar ta soke daya daga cikin hukuncin daurin rai da rai guda biyu da aka zartarwa Mohamed Morsi wannan na zuwa bayan soki wani hukuncin kisa akan tsohon shugaban kasar.

Tsohon Shugaban Masar Mohammed Morsi
Tsohon Shugaban Masar Mohammed Morsi DR
Talla

Kotun ta bukaci a sake shari’ar, kamar yadda lauyan da ke kare Morsi ya tabbatar.

Kotun kuma ta soke hukuncin da aka zartarwa mambobin kungiyar ‘yan uwa musulmi da dama da ake shari'arsu tare da tsohon shugaban akan zargin mika bayanan sirrin Masar ga Iran da kuma kungiyar Hamas ta Falasdinawa.

Morsi dai shi ne shugaban dimokuradiya na farko a Masar wanda al’ummar kasar suka zaba bayan kawo karshen zanga-zangar da ta kifar da gwamnatin Hosni Mubarak a 2011.

Amma shugaba na yanzu Abdel Fattah al Sisi ne ya hambarar da gwamnatin Morsi a lokacin da yana babban hafsan sojan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.