Isa ga babban shafi
Faransa

Sabon sansanin ‘yan gudun hijra na maza zalla a Paris

A yau Alhamis aka bude sabon sansani na ‘yan gudun hijira a birnin Paris don bai wa maza zalla mafaka, shirin na cikin matakan da Faransa ke dauka na sauya wa ‘yan gudun hijrar da ta kwashe daga sansani Calais matsuguni.

Wasu 'yan gudun hijra da aka kwashe daga sansanin Calais.
Wasu 'yan gudun hijra da aka kwashe daga sansanin Calais.
Talla

An kafa sabon sansanin ne a kusa da wani layin dogo da aka daina amfani da shi a tashar Gare du Nord, kuma yana iya daukan mutane 50-80 na adadin sabbin bakin haure dake shiga birnin Paris a kullum.

Hukumomin sun ce za a dau tsawon kwanaki goma ana gudanar da bincike da kuma bai wa ‘yan gudun hijrar magani da shawarwari musanman ga masu neman mafaka, kafin tsugunar dasu a cibiyoyin da aka ware musu.

A cewar Bruno Morel, shugaban wata gidauniyar ‘yan gudun hijira dake kula da sabbin cibiyoyin, an tsayar da wannan dabaru ne domin tabbatar da cewa duk wanda za a baiwa mafaka ya samu cikakken kulawa.

Sai dai za a kai farkon shekarar mai zuwa ta 2017, kafin a soma tsugunar da iyalai da mata a nasu sansani dake kudu maso gabanshin kasar da Ivry-sur-seine. Kana kananan yara da basu da kowa an ware musu nasu matsugunin.

Soma tsugunar da bakin maza zalla, na zuwa ne makonni bayan Jami’an tsaro sun rusa sansani da ‘yan gudun hijira dubu 3,800 ke samun mafaka a arewacin kasar, akasarinsu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.