Isa ga babban shafi
Najeriya

Manufofin Buhari akan inganta bangaren Man fetir

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar wasu manufofi guda bakwai domin inganta sashen man fetur da kuma iskar gas a kasar. Wasu daga cikin manufofin sun hada da samar da ci gaba a yankin Neja Delta da samar da tsaro a yankunan da ake hako mai da inganta matatun mai.

Karamin Ministan Man fetir kuma shugaban kungiyar OPEC Ibe Kachikwu
Karamin Ministan Man fetir kuma shugaban kungiyar OPEC Ibe Kachikwu REUTERS
Talla

A yayin kaddamar da tsarin a yau a Abuja, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce har yanzu bangaren man fetir ya kasance babbar hanyar samun kudaden Najeriya duk da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

An dai tsara shugaba Buhari zai gana da shugabannin al’ummomin yankin na Niger Delta mai arzikin mai a makon gobe.

Ministan mai na kasar Emmanuel Ibe Kachikwu, ya ce babbar manufar shirya ganawar ita ce, kawo karshen ayyukan tsagerenci da ke haddasa barna ga ayyukan man fetur wanda shi ne kashin bayan tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.