Isa ga babban shafi
Najeriya

Ayyuka na sun fi mukamin Jakada muhimmaci- Bugaje

Tsohon dan takarar gwamna a Jihar Katsina Dakta Usman Bugaje ya yi watsi da tayin mukamin shugaba Muhammadu Buhari na Jakada, inda ya ce hidimomin da ke gaban shi sun wadatar da shi.

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS
Talla

Dakta Bugaje ya fadi matsayinsa ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafin shi na facebook, inda ya yi godiya ga wadanda suke ganin ya cancanta da mukamin.

Amma ya ce yana da ayyuka da dama akan shi musamman aikin wata cibiyar raya arewacin Najeriya (ARDP).

“Na auna na gani kuma na yanke shawarar zama a gida domin ci gaba da gwagwarmayar tabbatar da shugabanci nagari” in ji Dakta Bugaje.

 

Sanarwar da Dr Bugaje ya fitar a Facebook

A makon jiya ne shugaba Buhari ya aike da sunayen mutane 45 zuwa majalisar dattawan kasar don tantance su a matsayin jakadun Najeriya a kasashen waje.

Amma yanzu Bugaje ya kasance mutum na biyu daga cikin mutanen 45 da suka yi watsi da tayin bayan tsohuwar mataimakiyar gwamnan Jihar filato Pauline Tallen ta yi watsi da tayin, tana mai cewa babu adalci wajen raban mukaman gwamnati a jiharta.

Watsi da tayin mukami a Najeriya dai sabon abu ne, amma wasu na ganin akwai wasu dalilai na daban da ya sa ake yin watsi da tayin mukaman na Shugaba Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.