Isa ga babban shafi
Najeriya

Tallen ta yi watsi da nadin da Buhari ya yi mata

Tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Plateau ta Najeriya, Pauline Tallen ta yi watsi da nadin da shugaba Muhammadu Buhai ya yi mata na jakadiyar kasar a waje, in da ta ce, babu adalci wajen raban mukaman gwamnati a jiharta.

Pauline Tallen, tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Plateau da ke Najeriya
Pauline Tallen, tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Plateau da ke Najeriya Wikistarz.com
Talla

Mrs. Tallen wadda ta taba rike mukamin ministar kimiya da fasaha da kuma tsaya takarar gwamnan Plateau karkashin jam’iyyar Labour a shekarar 2011, ta sanar da matakin da ta dauka a yau Litinin a birnin Abuja.

A cewarta, “ na fito daga karamar hukuma daya da gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong kuma na yi watsi da nadin ne saboda tabbatar da daidaito a nadin mukaman gwamnati”

Tsohuwar ministar ta ci gaba da cewa, ba a tuntubi gwamnan jiharta ba kafin yanke shawarar nada ta, domin kuwa ta zanta da shi ta wayar tarho a lokacin da ya ke Amurka amma ya tattabar mata cewa, ba shi dsa masaniya kan batun.

Sai dai ta ce, ita an tuntube ta amma ta yi watsi da tayin tun kafin ma a fitar da sanarwar nadin.

“Rashin lafiyar mai-gidana na daya daga cikin dalilan da suka tirsasa min watsi da tayin nadin.” In ji Tallen.

A makon jiya ne shugaba Buhari ya aike da sunayen mutane 45 ga majalisar dattawan kasar don tantance su a matsayin jakadun Najeriya a kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.