Isa ga babban shafi
DR Congo

Birtaniya ta goyi bayan kakabawa DR Congo takunkumi

Gwamnatin Birtaniya ta goyi bayan matakin Tarayyar Turai na kakabawa wasu jami’an gwamnatin DR Congo takunkumi domin kawo karshen Danniya da tabbatar ganin an samu sauyin gwamnati cikin kwanciyar hankali.

Shugaban kasar DR Congo Jospeh Kabila
Shugaban kasar DR Congo Jospeh Kabila REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Tuni dai Amurka ta kakabawa wasu manyan Jami’an soji da ‘yan sandan Congo takunkumi , yayin da a Turai kuma ra’ayi ya banbanta kan daukar matakin bai-daya a kasar da ke fama da rikicin siyasa sakamakon kudirin shugaba Joseph Kabila na zarce wa’adin shugabancinsa.

Faransa ce dai ta bukaci sauran mambobhin kasashen Turai su bi sahun Amurka na kakabawa manyan jami’an Congo Takunkumi, yanzu kuma Birtaniya ta bayyana goyon bayan matakin.

Daruruwan mutane ne dai suka mutu a arangama tsakanin masu zanga-zanga da Jami’an tsaro. Masu zanga zangar na adawa ne da matakin shugaba Kabila na kankanewa kan mulki bayan wa’adin shugabancinsa ya kawo karshe.

Kasashen na Turai na ganin Takunkuman dai zai yi tasiri matuka a kan shugabannin na Congo musamman haramta masu taba kadarorinsu da suke ajiya a Turai.

Shugaba Kabila dai na take taken dage zaben kasar ne da za a gudanar a watan nuwamban bana inda Majalisar Dinkin Duniya ke fargaba a kan yiyuwar ballewar yakin basasa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.