Isa ga babban shafi
Najeriya

DSS ta saki Alkalan da ta tsare

Hukumar ‘Yan sanda DSS ta saki dukkanin Alkalan da ta cafke a wani samamen da jami’anta suka kaddamar na yaki da rashawa akan manyan Alkalan.  Rahotanni sun ce hukumar ‘Yan sandan na farin kayan ta bayar da belin Alkalan ne wadanda za ta ci gaba da bincike akansu.

Nigerian state security service
Nigerian state security service dss
Talla

A yau Talata ne Majalisar Alkalan Najeriya ke gudanar da taro na musamman sakamakon dirar mikiyar aka kai wa wasu manyan Alkalan kasar a daren Juma’a inda ‘Yan sandan farin kaya suka ce sun kwato Miliyoyan daloli a farmakin da suka kai gidajen Alkalan.

Kaddamar da farmaki akan Alkalan dai ya janyo cece-kuce a Najeriya inda kungiyar Lauyoyi da Jam’iyyar adawa ta PDP suka yi allawadai da matakin wanda tare da sukar gwamnatin Buhari.

Alkalan da aka cafke sun hada da na Kotun Koli guda biyu da na Babbar Kotu a Abuja da wasu Jihohin Najeriya.

Babbar Alkalin Alkalan Najeriya Mahmud Muhammad ya yi allawadai da samamen wanda zai jagoranci taron Majalisar Alkalai a yau Talata a Abuja.

Majalisar Alkalan dai ta ki ba hukumar SSS hadin kai domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da Alkalan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.