Isa ga babban shafi
Najeriya

DSS ta yi wa gidajen wasu Alkalai dirar mikiya

Hukumar ‘Yan sandan farin kaya a Najeriya ta ce ta samu makudan kudade a gidajen alkalan da Jami’anta suka yi wa dirar mikiya a Abuja da wasu jihohi guda shida. Rahotanni sun ce ‘Yan sandan sun cafke Alkalan kotun koli guda biyu mai shari’a Okoro da Mai Shari’a Sylvanus Ngwuta.

'Yan Sandan Farin kaya a Najeriya
'Yan Sandan Farin kaya a Najeriya guardian
Talla

Alkalan da DSS ta kai wa farmakin sun hada da na kotun koli da kotun daukaka kara da kuma na babbar Kotu a Jihohin Kano da Sokoto da Gombe da Enugu da Fatakwal a kuma birnin Tarayya Abuja.

A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai Jami’in hukumar ta DSS Abdullahi Garba ya ce sun kaddamar da farmakin ne akan alkalan kan zargin cin hanci da rashawa.

Alkalan sun hada da na kotun koli guda biyu da na babbar kotu a Abuja da kuma mai shari’a Mu’azu Pindiga da aka yi wa dirar mikiya a gidansa da ke Gombe.

Sai dai gwamnatin jihar Rivers ta hana wa ‘yan sandan farin kayan shiga gidan alkalin babbar kotun Fatakwal Muhammad Liman. Mista Garba ya ce sun samu bayanin cewa alkalin ya mallaki kudi dala miliyan biyu.

Hukumar DSS ta ce ta kwato kudade na Naira da na kasashen waje.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.