Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Za'a sallami ma'aikatan gwamnati 25,000 daga aiki a Zimbabwe

Gwamnatin Zimbabwe ta jaddada cewa zata sallami ma’aikata 25,000 domin ceto bitalmalin gwamnatin kasar daga durkushewa.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe Reuters/Philimon Bulawayo
Talla

A gefe guda kuma gwamnatin ta ce ma'aikatan da za'a bari zasu rika karbar tagomashin albashi na karshen shekara, duk bayan shekaru biyu.

Sanarwar tazo bayan Ministan kudin kasar ta Zimbabwe, Patrick Chinamasa a ranar Juma’ar da ta gabata, ya bayyana cewa albashin ma’aikatan kasar yana lashe kimanin kashi 96% cikin 100% na kasafin kudin gwamnati.

A cewar Chinamasa ko a watanni shida na farkon wannan shekara, sai da gwamnatin kasar ta samu gibin dala miliyan 623 a kasafin kudinta, zuwa karshen shekara kuma akwai hasashen sake samun gibin dala biliyan daya a kasafin kudin na Zimbabwe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.