Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Zanga zanga ta rikide zuwa tarzoma a Zimbabwe

Shugaba Robert Mugabe yayi kaukausar suka kan alkalan kasar da suka baiwa ‘yan adawa izinin gudanar da zanga zangar da ya rikide zuwa tarzoma.

Masu zanga zangar na adawa da mulkin Mugabe don halin matsin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Masu zanga zangar na adawa da mulkin Mugabe don halin matsin da tattalin arzikin kasar ke ciki. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Shugaba Mugabe wanda ya bayyana alkalan a matsayin marasa hankali yace yana fatan sun fahimci illar da suka yi ganin yadda masu zanga zangar suka tada hankalin jama’a.

Tabarbarewar tattalin arziki da rashin aikin yi musanman a tsakanin matasan kasar na daga cikin dalilan da suka harzuka 'yan adawa gudanar da zanga zangar.

‘Yan adawar sun samu izinin zanga zanga ranar 26 ga watan jiya wadda ta haifar da arangama tsakaninsu da ‘Yan Sanda, al’amarin ya kaiga kama 70 daga cikin su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.