Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Kotu ta dage haramcin zanga zanga a Zimbabwe

Rahotannin a yau Laraba sun ce babbar kotun kasar Zimbabwe, ta dage haramcin gudanar da zanga zanga a babban birnin kasar Harare da hukumar ‘yan sandan kasar ta kafa.

Zanga zangar adawa da gwamnatin shugaban Zimbabwe Robert Mugabe
Zanga zangar adawa da gwamnatin shugaban Zimbabwe Robert Mugabe DR
Talla

Yanzu haka dai gamayyar jam'iyyun adawar kasar sun yi maraba da wannan mataki na babbar kotun kasar.

A baya Jamiyyun adawa a Zimbabwe sun zargi gwamnatin kasar da gallazawa al-umma, bayan haramta musu damar gudanar da zanga zanga da kuma kamen da tsaro ke yi na babu gaira babu dalili.

Saidai kuma yayinda take maida martani kan wannan zargi, rundunar yan sandan Zimbabwe ta ce daukar matakin hana jerin zanga zangar ya zama dole domin hakan zai iya haifar da hare-haren ta-addanci a kasar.

Wani mai magana da yawun yan sandan kasar Manzini Moyo, yace suna da rahoton cewa wasu kungiyoyin 'yan ta-adda sun fara sawa kasar idanu ganin halin da take ciki na karuwar tashe tashen hankula saboda zanga zangar nun kin jinnin gwamnatin Mugabe da –yan adawa ke yi.

A cewar Moyo akwai shirin kaiwa gidajen yarin kasar hari domin fito da fursunoni.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.