Isa ga babban shafi
Habasha

Gobara ta hallaka mutane 23 a Habasha

Rahotanni daga kasar Habasha sun ce akalla mutane 23 suka mutu sakamakon wata gobarar da ta tashi a wani gidan yarin kasar da ke dauke da fursinonin siyasa a Adis Ababa.

Talla

Gwamnatin kasar ta tabbatar da mutuwar mutane 21 sakamakon shakar hayaki, yayin da wasu biyu kuma suka mutu sakamakon turmitsitsin da aka samu lokacin da suke kokarin tserewa.

Kafofin yada labaran kasar sun ce anji karar harbe harbe lokacin da aka samu gobarar da har yanzu aka gaggara gano musababbin wutar.

Akasarin wadanda ke zama a gidan yarin, mutane ne da aka cafke lokacin wata Zanga-zangar adawa da gwamantin a watanni baya.

Hukumar kare hakkin bil'adama, HRW, ta kiyasata kashe sama da mutane 400 a Zanga-zangar  da jami'an tsaro sukayi arangama da mutane a watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.