An yi zanga-zangar adawa da gwamnatin Habasha
Jami’an ‘yan sandan Habasha sun kama mutane da dama a wata zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar da suka gudanar a birnin Addis Ababa a wannan asabar.
Wallafawa ranar:
Kungiyoyin ‘yan adawa daga gungun kabilun Oromo da ke da yawan al’umma ne suka shirya zanga-zangar, inda mutane kimanin 500 suka yi gangamni a dandalin Meskel tare da fadin cewa, suna bukatar gwamnati ta basu ‘yancinsu, sannan kuma ta sake musu ‘yan siyasar da aka garkame a gidan-kaso.
A ranar juma'a ne Firaministan kasar Haile Mariam Dessalegn ya haramta gudanar da zanga-zangar wadda ya bayyana a matsayin baraza ga zaman lafiyar kasar ta Habasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu