Isa ga babban shafi
Habasha-Sudan

Habasha na zaman Makokin kwananki Biyu

Al’ummar kasar Habasha sun soma zaman makoki na kwanaki biyu don jimamin ‘Yan kasar 208 da aka kashe a makon da ya gabata.

'Yan bindiga Sudan sun kashe mutane 208 a yammacin Ethiopia
'Yan bindiga Sudan sun kashe mutane 208 a yammacin Ethiopia
Talla

Al’amarin dai ya auku ne a yankin Gambela bayan arangama tsakanin makiyayan kasar Sudan ta Kudu dake makwabataka da kasar ta Habasha.

Gwamnatin kasar ta ce akwai kuma wasu yara 100 da aka yi garkuwa dasu a yayin rikicin ba tare da yin Karin bayanin ko ina aka kwana a binciken gano yaran ba .

Firaministan Hailemariam Desalegn ya ce gwamnati na aiki da hukumomin kasar Sudan don gano wadanda suka kai wannan kazamin harin don hukuntasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.