Isa ga babban shafi
Afrika

Giwa na karewa a Afrika

Wani Bincike da aka kwashe shekaru uku ana yi ya nuna cewar adadin Giwayen da ake da su a nahiyar Afirka sun ragu da kashi 30 saboda yadda ake ci gaba da hallaka su ana safarar haurensu.

Giwaye na karewa a kasashen Afrika
Giwaye na karewa a kasashen Afrika WikiCommons/Gary M. Stolz/U.S.
Talla

Attajiri Paul Allen, daya daga cikin shugabannin kamfanin Microsoft ya bada gudumawar Dala miliyan 7 domin gudanar kidiyar giwayen, sakamakon da ya jefa fargaba musamman ga masu kare hakkokin dabbobi.

Mista Allen ya ce sakamakon binciken ya nuna cewar dole a dauki matakin gaggawa domin kare lafiyar gandun dawa 352,271 da ke neman karewa.

Kasashen da matsalar ta fi kamari sun hada da Afirka ta kudu da Botswana da Uganda da Kenya da Zambia da Zimbabwe da Malawi.

Wannan ne karon farko da aka gudanar da kidayar gandon dajin a kasashe 18 na Afrika wanda aka soma tun a watan Disemban 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.