Isa ga babban shafi
Nijar

Rashin kudi na barazana ga aikin yaki da Tamowa a Nijar

Hukumar samar da tallafin abinci ta majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa karancin kudi na iya dakatar da aikin yaki da tamowa ga yara kanana a Nijar.

Yara na fama da Tamowa a Nijar
Yara na fama da Tamowa a Nijar AFP/BOUREIMA HAMA
Talla

Hukumar ta ce rashin kudin na yin barazana ga dukkanin ayyukanta inda sama da yara hudu cikin 10 ke fama da tamowa a Nijar.

Sannan hukumar ta ce yawan tallafin abincin da ta ke bayarwa ya ragu kuma yanzu aikin baki daya zai tsaya ne daga watan Satumba saboda rashin kudi.

Hukumar samar da tallafin ta ce tana bukatar kudi kusan dala miliyan 21 da rabi domin gudanar da ayyukan jin-kan daga watan Satumba zuwa Disemba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.