Faransa Ta Kori Soja Biyar Saboda Hannu Wajen Ayyukan Hashsha a Janhuriyar Africa
Kasar Faransa ta hukunta wasu sojan kasar biyar wadanda ke da hannu wajen cin zarafin mutane yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Janhuriyar Africa ta Tsakiya.
Wallafawa ranar:
Ma'aikatar Tsaro ta Faransa ta sanar da daukan wannan hukunci yau Asabar.
Ma'aikatar ta fadi cewa saboda girman zargin da ake yiwa sojan an dakatar dasu, kuma za’a dauki wasu matakan ladabtarwa da koran kare daga aikin sojan kasar Faransa.
Kasar Faransa ta jagoranci tura sojan ta zuwa kasar Janhuriyar Africa ta Tsakiya domin aikin wanzar da zaman lafiya, bayan barkewar rikicin kabilanci da na addini da yayi sanadiyyar mutuwar dimbin mutane a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu