Isa ga babban shafi
Afrika taTsakiya

Zaben CAR: 'Yan takara sun goyi bayan kidayar kuri'u

‘Yan takarar shugabancin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun goyi bayan hukumomin kasar da su ci gaba da aikin kidayar kuri’un zaben da aka gudanar a karshen shekarar bara, kamar yadda rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar dinkin duniya ta sanar.

'Yan takarar 28  na Afrika ta Tsakiya sun goyi bayan ci gaba da kidayar kuri'un zaben kasar
'Yan takarar 28 na Afrika ta Tsakiya sun goyi bayan ci gaba da kidayar kuri'un zaben kasar MARCO LONGARI / AFP
Talla

A yanzu dai ‘yan takara 28 daga cikin 30 ne suka amince da ci gaba kidayar da kur’un duk da cewa a baya, 20 daga cikin su sun bukaci a soke aikin kidayar bayan sun yi zargin cewa an tafka kura kurai a zaben amma hukumomin kasar suka yi watsi da bukatar.

An dai kidaya kimanin kashi 77 cikin 100 na kuri’un da aka kada a ranar 30 ga watan Disamban bara a zaben da ake ganin zai kawo karshen tashin hankalin da kasar ta tsinci kanta a ciki shekaru uku da suka gabata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban jama’a.

Tsoffin firaministocin kasar biyu na kan gaba wajan samun yawan kuri’u, abinda zai  ba su damar shiga zagaye na biyu na zaben wanda za a gudanar a ranar 31 ga wannan watan na Janairu.

Anicet George Dologuele na da kuri’u 259,211 yayin da Faustin Archange Touadera ke da kuri’u 222,391.

Baya ga wadannan tsoffin ministocin babu wani dan takara da ya samu sama da kuri’u 135,000.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.