Isa ga babban shafi
Afrika taTsakiya

Afrika ta Tsakiya ta yi watsi da bukatar 'yan takara

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ce, babu dalilin dakatar da ci gaba da kidaya kuri’un zaben shugaban kasar da aka yi sakamakon korafin da wasu 'yan takara 20 suka gabatar.

Kasashen Turai da na Afrika sun taka rawar gani don ganin an gudanar da ingantaccen zabe a Afrika ta Tsakiya.
Kasashen Turai da na Afrika sun taka rawar gani don ganin an gudanar da ingantaccen zabe a Afrika ta Tsakiya. MARCO LONGARI / AFP
Talla

Ministan cikin gida Modibbo Bachir Walidou ya ce za a ci gaba da kidaya kuri’un kamar yadda aka shirya.

A ranar litinin da ta gabata ne 'yan takara 20 daga cikin 30 suka bukaci a soke zaben bayan sun yi zargin cewa an tafka magudi, yayin da shugaban hukumar zaben kasar Julius Ngouade Baba, ya ce ba za su dakatar da aikin da suke kan gudanarwa ba.

Tuni aka fitar da wani sashi na sakamakon zaben farko  kuma ana sa ran gudanar da zabe na biyu a ranar 31 ga watan Janairun da muke ciki.

Shi ma firaministan kasar Mahamat kamoun ya bukaci 'yan takarar da su mayar da hankali kan bukatar kasar.

Sannan ya ce, hukumomin Afrika ta Tsakiya da kungiyoyin tarayyar Turai da na Afrika har ma da Faransa da Amurka da China duk sun taka rawar gani domin tabbatar da cewa an gudanar da ingantaccen zabe a kasar.

Ana dai sa ran zaben na shugaban kasa da ‘yan majalisu zai taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya bayan ta shafe shekaru uku a cikin rikici.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.