Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Africa ta Tsakiya

Zaben CAR: Dologuele da Touadera za su kara a zagaye na 2

Tsoffin Firminista Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya biyu, Ancient Georges da Fausrin Archanbe Touadera ke kan gaba wajen samun yawan kuri’u, lamarin dake nuna cewa su za suje zagaye na biyu a zaben Shugabanci kasa da ake sa ran gudanarwa a ranar 31 ga wannan watan na Janairu.

Akwatina Zabe a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Akwatina Zabe a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Rahotanni sun ce Anicet Georges Dologuele na da kashi 23.78 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada a zagaye na farko, yayin da Archange Touadera ke da kashi 19.42 cikin 100, sai dai zuwa yanzu hukumar zaben kasar ba ta bada sanarwa a hukumace ba.

Dologuele tsohon ma’aikacin babban bankin kasa mai shekaru 58, a kan masa lakabi da tsafta, sakamakon wani yunkuri na tsafttace asussun gwamnati da ya yi a lokacin da ya ke Premier kasar tsakanin 1998-2001.

Shi kuwa Touadera mai Shekaru 58, Ferfessa lissafi ne, kuma ya yi Premier ne karkashin gwamnatin tsohon shugaba Francois Bozize

Hukumar zaben kasar ANE ta ce kashi 69 cikin 100 na al’ummar kasar ne suka fito kada kuri’u shugabanci kasa da na 'yan majalissun dokoki.

Akalla kusan mutane miliyan 2 cikin miliyan 5 na adadin al’ummar kasar ne ke da daman kada kuri’u, a zaben da ake gani zai bude sabon babi samar da zaman lafiya a kasar da aka shafe shekaru 3 babu kwanciyar hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.