Isa ga babban shafi
CAR

Yau ake rantsar da Touadera shugaban kasar CAR

A yau laraba ake rantsar da Faustin Touadera a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bayan nasarar da ya yi a zaben da aka gudanar a cikin watan jiya.

Sabon shugaban kasar Afrika ta Tsakiya  Faustin Touadéra.
Sabon shugaban kasar Afrika ta Tsakiya Faustin Touadéra. RFI/Matéo Guidoux
Talla

Touadera mai shekaru 58 a duniya zai karbi ragamar mulkin wannan kasa ce da ta share tsawon shekaru tana fama da tashe-tashen hankula da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma rabuwar kawuna a tsakanin kabilu da kuma mabiya addinai.

Bayan faduwar gwamnatin tsohon shugaba Francois Bozize a shekara ta 2013, yakin basasa ya barke a kasar wanda daga bisani ya rikide ya zama rikici tsakanin musulmi da kuma Kirsta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu tarin yawa, yayin da wasu fiye da dubu 400 suka guje wa gidajensu.

Manazarta dai na ganin cewa akwai gagarumin aiki a gaban sabon shugaban wajen sake dinke barakar da aka sama a tsakanin al’umma, yayin da tattalin arzikin kasar ya samu mummunan koma-baya a cikin wadannan shekaru na tashe-tashen hankula.

Ana sa-ran tawagogi daga kasashen duniya ciki har da Faransa da ma Majalisar Dinkin Duniya za su halarci bikin rantsar da sabon shugaban wanda zai gudana a birnin Bangui.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.