Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da zaben da aka yi a Afrika ta Tsakiya
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin kwanciyar hankali, inda ya bukaci shugabannin kasar da su tabbatar da dorewar zaman lafiya.
Wallafawa ranar:
Ban wanda ya aike da sakon taya murna ga Faustin-Archange Touadera sakamakon nasarar da ya samu kamar yadda rahotanni suka nuna, yace nasarar zata bada damar ci gaba da sasanta tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna.
Touadera wanda tsohon malamin jami’a ne kuma tsohon Firaminista ya samu kashi 60 na kuri’un da aka kada.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu