Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

An soma kidayar kuri'un zaben Afrika ta Tsakiya

Jami’an Hukumar zabe a kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun fara kidaya kuri’un zaben raba gardamar shugaban kasar da akayi jiya lahadi.Ana fafatawa ne tsakanin Anicet Georges Dologuele da Faustin Archange Touadera wadanda suka taba rike mukamin Firaminista a baya. 

wani dan kasar Afrika ta Tsakiya dake jefa kuri'ar sa cikin akwatin zabe
wani dan kasar Afrika ta Tsakiya dake jefa kuri'ar sa cikin akwatin zabe ISSOUF SANOGO/AFP
Talla

Zaben na jiya dai wata dama ce da al’ummar kasar suka samu na zabin shugaban da suke ganin zai hada al’ummar kasar da kuma kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe dogon lokaci anayi.
Kasashe da dama ne suka tura wakilai da za su sa ido a zaben kasar,Gwamnatin kasar bisa shugabancin Uwargida Catherine Samba Panza ta yi kira zuwa daukacin yan kasar na gani sun kaucewa duk wani tashin hankali da kan iya haifar da yamuci a wannan sabuwar tafiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.