Farfesa Faustin-Archange ya zama Shugaban Kasar Janhuriyar Africa
Al'ummar kasar Janhuriyar Tsakiyar Africa sun sami sabon Shugaban kasa bayan babban zaben kasar da akayi ba dadewa.Sabon Shugaban kasar Shine Faustin-Archange Touadera,mai shekaru 58, tsohon Fira Minista kuma Malamin darasin lissafi, wanda ya tsaya a matsayin dan takara na indifenda.
Wallafawa ranar:
Hukumar zaben kasar ta sanar da cewa ya sami kashi sittin da biyu daga cikin dari na yawan kuri'u da aka jefa.
Mai bi masa shine Anicet-George Dologuele wani tsohon ma'aikacin Banki wanda ya sami yawan kuri'u kashi 37 daga cikin dari na yawan kuri'u da aka jefa.
A zagayen farko ya baiwa mutan kasar mamaki kasancewar shine yazo na biyu a zaben.
Ya kasance mutan kasar na matukar girmamashi a matsayin malamin darasin lissafi wanda yayi karatu har ya zama Farfesa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu