Isa ga babban shafi
Afrika

"Za mu kalubalanci hukuncin kotu a kan Jacob Zuma"

Masu shigar da kara na gwamnatin Afrikla ta kudu sun bayyana cewa, za su kalubalanci hukuncin da babbar kotun kasar ta yanke kan shugaba Jacob Zuma, inda ta bukaci a tuhume shi kan zarge-zarge kusan 800 masu nasaba da cin hanci da rashawa.

Jacob Zuma na Afrika ta kudu
Jacob Zuma na Afrika ta kudu REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Darektan hukumar shigar da kara ta kasar, Shaun Abrahams ya sanar da kudirinsu, yayin da ya musanta zargin fuskantar matsin lambar siyasa.

Shugaba Zuma ya shafe watanni yana shan caccaka, inda al’mmar kasar suka bukaci ya sauka daga mukaminsa saboda zargin sa da almundahana a dai dai lokacin da kasar ke fama da matsalar tattalin arziki da kuma rashin ayyukan yi tsakanin matasa.

A shekarar 2009 ne, aka janye tuhumar da ake yi wa Mr. Zuma ta biliyoyin Dala, abinda ya ba shi damar tsayawa takara har ya lashe zaben shugabancin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.