Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

An yi zafi a Maris din bana fiye da sauran Maris

Watan Maris din bana da ya gabata ya kasance mafi tsananin zafi da aka taba gani a wannan zamanin wanda shi ne karo na 11 a watannin da aka samu zarcewar ma’aunin yanayin tsananin zafi a sassan kasashen duniya.

Mutane na sanyaya jikinsu da ruwa a rafi a Islamabad kasar Pakistan saboda tsananin zafi
Mutane na sanyaya jikinsu da ruwa a rafi a Islamabad kasar Pakistan saboda tsananin zafi Reuters
Talla

Hukumar da ke kula da Yanayi a Amurka ta ce watan Maris din bana ya kasance wata mafi tsananin zafi a tarihin watanin Maris cikin shekaru 137 da suka gabatam kusan a wajajen 1880.

Hakan dai ya faru ne sakamakon dumamar yanayi a duniya.

Rahotan ya bayyana cewa zafin ya fi tsananta a gabashin Brazil, da gabashi da tsakiyar Afrika da kuma kudu maso gabashin yankin Asia da mafi yawa daga cikin yankunan arewa da kuma gabashin Australia.

A Arewa maso yammacin Canada da arewa da kuma yamamcin Asia an samu karin maki 3 na matsakaicin yanayi.

Rahoton binciken ya ce a Australia a karon farko cikin shekaru 107 an yi zafi mai tsanani, kamar yadda aka samu zafi sosai a kasashen Sweden da Denmark da kuma Norway.

Sai dai kuma a kasashen Faransa da Britaniya yanayin zafin ya ragu sabanin matsakaicin ma’auninsu daga shekarun 1981 zuwa 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.