Afrika ta Kudu
Za a fara muhawarar tsige Jacob Zuma
Majalisar dokokin Afrika ta Kudu za ta fara mahawara kan bukatar tsige shugaban kasar Jacob Zuma a gobe Talata.
Wallafawa ranar:
Talla
Wannan dai na zuwa ne bayan babbar kotun kasar ta same shi da laifin taka kundin tsarin mulki wajen amfani da kudin talakawa domin fadada gidansa.
Shugaban majalisar Baleka Mbete ne ya sanar da zaman muhawarar sakamakon hukuncin na kotun da ta umurci Zuma ya mayar da wani kaso na Dala miliyan 16 da ya yi amfani da su cikin kwanaki 45 masu zuwa.
Mmusi Maimane, shugaban Jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance ya gabatar da kudirin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu