Isa ga babban shafi
South Africa

Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma Ya Nemi Gafarar Mutan Kasar Sa

Shugaban kasar Africa ta kudu Jacob Zuma ya musanta zargin da ake yi masa na amfani da kudaden Gwamnatin ba bisa ka'ida ba wajen gyatta gida na kan sa.

Shugaba Jacob Zuma na Africa ta Kudu
Shugaba Jacob Zuma na Africa ta Kudu rfi
Talla

Musanta zargin na zuwa bayan da wata kotun kasar ta nuna abin kunya ne kuma ya ci shugaban ya sauka daga mulki.

Wannan zargi ya kasance mafi kidima shugaban wanda yasha suka a baya saboda zarge-zarge na cin hanci da rashawa, har ma da zargin fyade da ake yi masa.

Shekaranjiya Alhamis wata kotu ta ce Shugaba Jacob Zuma ya kasa mutunta kundin tsarin mulki, tunda yayi kunnen uwar shegu da umarnin kotu na ya maida kudade Dollan Amirka miliyan 16 da ake zargi yayi amfani dasu ba bisa kaida ba wajen gyatta gidan sa.

Daga bisani dai ya nemi gafarar mutan kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.