Isa ga babban shafi
Central Africa

An Rantsar da Faustin-Archange Touadera Shugaban Africa ta Tsakiya

Sabon shugaban kasar Janhuriyar Africa ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera ya yi alkawarin tabbatar da dorewar zaman lafiya a fadin kasar.  

Sabo shugaban kasar Africa ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra
Sabo shugaban kasar Africa ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra (Photo : AFP)
Talla

Sabon Shugaban na magana ne yau Laraba a lokacin da yake rantsuwar kama aiki.

Yayi fatan ganin yana mutunta kundin tsarin mulki da tafiyar da harkokin kasar ba tare da nuna wani banbanci ba.

Anyi bukin rantsuwar ne a filin wasanni dake birnin Bangui inda shugabannin kasashen duniya da wakilai dama suka halarta.

Cikin shugabannin da suka halarta akwai Shugaban Guinea Teodoro Obiang Nguema, da Shugaban Guinea Denis Sassou Nguesso da Ministocin tsaro na Faransa da takwaransa na Harkokin waje.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.