Isa ga babban shafi
FRANCE- CAR

Faransa na Shirin Janyewa Daga Janhuriyar Africa

Gwamnatin Faransa za ta janye dakarunta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya, yayin da ta cimma burinta na maido da tsaro a kasar wadda ta shafe shekaru uku ta na fama da tashe -tashen hankula.

Ministan Tsaro na Faransa Jean-Yves Le Drian
Ministan Tsaro na Faransa Jean-Yves Le Drian REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian ya bayyana haka a wannan Laraba a Birnin Bangui , inda ya tabbatar cewa rundunar ta Faransa da ake kira Sangaris za ta kawo karshen zamanta a Afrika ta Tsakiya a cikin wannan shekara, sai dai bai fadi takamanman ranar da za ta fice ba.

Faransa ta kaddamar da rundunar ne a watan Disamban shekarar 2013, a dai dai lokacin da dubban al’ummar Musulmi da Kirsita suka rasa rayukansu sakamakon tarzoma.

Mr. Le Drien ya ce, rundunar ta maido da zaman lafiya a kasar tare da dakile abubuwan da ba a amince da su ba.

To sai dai miinistan ya ce, kasar ba ta gama gyagijewa ba amma dai tana ci gaba da farfadowa daga rikicin wanda ya daidaita ta.

Kasar dai ta tsunduma cikin tsahe- tashen hankula ne a watan Maris na shekarar 2013, a lokain da ‘yan tawayen Seleka mafi yawan su musulmai suka kifar da gwamnatin Francois Bozize, sanna kuma suka dora shugabansu Michel Djotodia, wanda ya zauna kan karagar mulki na tsawon watanni 10.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.