Isa ga babban shafi
Rwanda, UN

Wani Sojan Rwanda da ke Kasar Janhuriyar Tsakiyar Africa ya Kashe abokan aikin sa biyar

Wani sojan kasar Rwanda dake cikin ayarin dake wanzar da zaman lafiya a kasar Janhuriyar Tsakiyar Africa ya bude wuta kan abokan aikin nasa  inda nan take ya kasha soja hudu kafin daga bisani ya kashe kansa. 

Ayarin sojan wanzarda zaman lafiya na Rwanda da ke Bangui
Ayarin sojan wanzarda zaman lafiya na Rwanda da ke Bangui AFP PHOTO / Pacome PABANDJI
Talla

Akwai kuma wasu sojan takwas da ya jikkata, kafi ya kashe kansa.

Bayanai na nuna kafin wayewar gari  Asabar lamarin ya auku.

Mai magana da yawun sojan wanzar da zaman lafiya a Bangui,  Manjo-Janar Joseph Nzabamwita ya bayyana cewa suna binciken wannan alamari kafin su dauki matakin daya dace.

Dakarun dake wanzar da zaman lafiya a kasar Janhuriyar Africa ta Tsakiya sun kai 10,800 da suka fito daga kasashen Burundi, Cameroon, Congo,Janhuriyar Democradiyya ta Congo , Equitorial Guinea, Gabon, Rwanda, Morocco, Senegal, Pakistan da Indonesia.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.